Halarcin zanga-zanga: 'Yan shi'a sun kada 'yan sanda a kotun garin Sokoto
Babbar kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Sokoto a jiya Laraba ta yanke hukunci game da karar da wasu 'yan shi'a a garin suka shigar a gaban ta suna kalubalantar hana su yin taron gangamin su a jihar a watannin baya.
To sai dai da alkalin kotun Mai shari'a Saleh Idrissa na yanke hukunci a kan karar, ya gargadi 'yan sandan jihar da su guji yi wa 'yan shi'ar shigar shigula a harkokin addinin su inda ba su karya doka ba.
KU KARANTA: Ku karanta labarin wani da ya bugi matar sa saboda zabe
Legit.ng ta samu cewa sai dai kuma kotun tayi fatali da bukatar 'yan shi'ar da suka ce kotun ta tursasa 'yan sandan su biya su diyyar Naira 50 miliyan.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa a jiya Laraba da tsakar dare wasu 'yan bindiga dadi fataken dare suka afkawa wani kauye da ake kira da Kaguru dake a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna inda kuma suka kashe akalla mutane shidda.
Mun samu dai cewa 'yan bindigar da ake kyautata zaton barayin shanu ne sun far ma kauyen da tsakar dare inda suka yi ta harbe-harben bindiga a sama kafin daga bisani su fatattki mutanen kauyen duka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng