Obasanjo ya ja ayarin jiga-jigan 'yan APC da PDP zuwa taron kaddamar da kungiyar kada Buhari
- Obasanjo ya ja ayarin jiga-jigan 'yan APC da PDP zuwa taron kaddamar da kungiyar kayar da Buhari
- Manyan 'yan siyasar da suka halarci bukin kaddamarwar sun fito ne daga jam'iyyu daban daban
- Satin da ya gabata ne Obasanjo ya rubutawa shugaba Muhammadu Buhari wasika
Labarin da muke samu yanzu yanzu da dumin sa na tabbatar mana da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar watau Cif Olushegun Obasanjo ya ja wani ayarin manyan manyan 'yan siyasar Najeriya daga jam'iyyun daban daban ya zuwa kaddamar da sabuwar kungiyar sa.
KU KARANTA: Masu kudi sun fara gudu daga Legas saboda haraji
Mun samu dai daga majiyoyin mu cewa manyan 'yan siyasar da suka halarci bukin kaddamarwar sun fito ne daga jam'iyyu daban daban na kasar nan ciki kuwa hadda APC mai mulki da PDP mai adawa.
Legit.ng ta samu dai cewa a cikin satin da ya gabata ne tsohon shugaban kasar ya rubutawa shugaba Muhammadu Buhari doguwar wasika yana shawartar sa da kar ya tsaya takarar tazarce a zabe mai zuwa.
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Zamfara a yau din nan ranar Alhamis, 1 ga watan Fabreru ta yi kaca-kaca da Sanata daga jihar mai wakiltar jihar Zamfara ta tsakiya watau Sanata Kabiru Marafa game da kalaman sa game da batun tsaro a jihar.
Wani mai ba wa Gwamnan shawara ne mai suna Alhaji Salisu Isah yayi masa kaca-kaca din a garin Kaduna lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng