Masu kudi sun fara barin jihar Legas saboda yawan haraji da suke biya - Rahoto
- Yawan haraji yasa masu kudi sun fara barin jihar Legas
- Rahotanni sun nuna attajiran dake barin jihar Legas suna komawa Dubai da Aukland
Masu kudi da sun fara barin jihar Legas saboda yawan harajin da suke biya, wanda hakan ya hana su samun riba a kasuwanci da suke yi a jihar.
Rahatannnin sun nuna jihar Legas, birnin Landan da Instanbul suna fuskantar matsalar ficewar masu kudi daga cikin su.
Rahoton ya nuna attajiran dake barin birnin Landan da jihar Legas suna komawa Dubai da birnin Aukland.
Ficewan attajirai daga gari matsala ce ga siyasa da tattalin arzikin kasar.
KU KARANTA : Gwamnaonin Najeriya karnuka ne mara sa hakura - Ishaku
Rahotanni sun nuna birnin Aukland, Dubai, New York, Tel Aviv da Toronto suna ganin shigowar masu kudi sosai.
Attajiran ‘yan kasar Sin, India suna zuwa kasar Amurka da Canada, sai kuma ‘yan kasar Rasha suna zuwa kasar Birtaniya da Cyprus.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng