Tsohon babban hafsan rundunar Sojan ruwa ya sulala ya mayar ma hukumar naira miliyan 600 da ya sata

Tsohon babban hafsan rundunar Sojan ruwa ya sulala ya mayar ma hukumar naira miliyan 600 da ya sata

Wani jami’in hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, yaa shaida ma babbar kotun babban birnin tarayya Abuja yadda tsohon babban hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Usman Jibrin ya gilla ma matarsa karya game da satar kudaden da yayi.

Daily Trust ta ruwaito jami’In na EFCC yaa fadin a zantawar da yayi da uwargidan Jibrin, ta shaida musu cewa Maigidanta tabbatar mata da cewa wani gida na naira miliyan 600 da ya mallaka a garin Abuja, an bashi ne a matsayin kyauta sakamakon ritaya da zai yi.

KU KARANTA: Taka leda: Najeriya ta doke kasar Sudan a gasar Afirka, ta tsallaka zuwa wasan karshe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jibrin tare da Rear Admiral Bala Mishelia da kuma Rear Admiral Shehu Ahmadu tare da wani kamfani Harbour Bay International Limited na fuskantar tuhume tuhume guda hudu da suka danganci satar kudaden rundunar sojan ruwa, wanda suka siya gidan Naira miliyan 600 dasu.

Tsohon babban hafsan rundunar Soja ruwa ya sulala ya mayar ma hukumar naira miliyan 600 da ya sata
Jibrin

Bugu da kari bincike ya nuna sunayen matar jibrin Hajiya Lami da dansa Abdulqadir a matsayin shuwagabannin kamfanin, kamar yadda aka yi ma kamfanin rajista, sai dai Lami tace ba ta da wata masaniya game da wannan gida, har sai a watan Janairun 2016 da mijinta ya fada mata wai kyauta aka ba shi.

Sai dai da bincike yayi zurfafa, shi kansa Jibrin ya musanta mallakar wannan gida, inda yace abokin aikinsa Shehu Ahmadu ne ya siyan masa gidan, kuma ya mika masa takardun gidan.

Nwoke Cyril, wanda shi ne jami’in EFCC dake gudanar da wannan bincike na kurilla, ya shaida ma Kotu cewa ya tuntubi babban hafsan sojan ruwa na yanzu, Ibok EKwe Ibas, wanda yace ya tuntubi jibrin da kansa, kuma ba tare da tambayarsa ba ma ya dawo ma hukumar da takardun gidajen.

Bayan jin ta bakin Cyril, sai Mai shari’a Salisu Umar y adage sauraron karar zuwa ranar 19 watan Feburairu da 8 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng