Duniya ta zo karshe: Wani Magidanci ya zakke ma wasu ƙannen matarsa ƙananan yara su 2, ɗaya ta yi ciki
Kotun Magistri dake garin Damaturu na jihar Yobe ta daure wani Magidanci mai shekaru 35 kan aikata lafiin fyade ga wasu yan mata guda biyu kanana, kannen matarsa, har daya ta samu ciki.
Dansanda mai shigar da kara, Sajan Hayatu Musa ya shaida ma kotu cewa uban yara, Malam Baba Ibrahim ne ya kai musu karar surukinsa mai suna Mohammed Baushe, mai inkiya Gareji da cewar yayi lalata da yayansa su biyu.
KU KARANTA: Taka leda: Najeriya ta doke kasar Sudan a gasar Afirka, ta tsallaka zuwa wasan karshe
Sajan Musa yace Gareji, wanda ya kasance yana zama ne gida daya da surukansa ya dade yana amfani da yan matan, tun suna kasa da shekaru 4, har zuwa yanzu da daya ta kai shekara 9, dayar kuma shekaru 12, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar NAIJ.om ta ruwaito har sai da aka gudanar da gwaji ka babbar, mai shekaru 12 ne aka gano tana dauke da ciki wata shida, kuma da ta ji matsa ta tona asirin wanda yayi mata cikin.
Sai dai da aka karanto ma wannan mutumin laifukan da ake tuhumarsa a kai, sai yayi wuf ba tare da bata ma kotu lokaci ba ya amsa laifukan nasa, wadanda sun saba ma sashi na 275 da 283 na kundin hukunta kananan laifuka.
Bayan sauraron dukkan bangarorin ne sai Alkali Abubakar Lamba ya bukaci a kara kawo masa hujjoji da zasu gamsar da Kotu cewa wanda ake zargi ya aikata wannan laifi, daga nan kuma y adage karar zuwa ranar 4 ga watan Feburairu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng