Mijina ya lakada min na jaki don kawai na fita yin zabe - Wata mata ta sanar da kotu

Mijina ya lakada min na jaki don kawai na fita yin zabe - Wata mata ta sanar da kotu

- Wata mata, Folasade Fatunla, ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta saboda sun samu sabani a kan zaben jihar Ekiti na 2014

- Matar ta shaidawa kotu cewar mijinta, Gbenga, ya jibge ta don kawai ta fita ta kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Ekiti

- Matar ta ce shekaru 12 suna zaune tare da mijin nata duk da bai biya kudin sadakinta ba

Wata mata, Folasade Fatunla, ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta, Gbenga, saboda ya lakada mata duka don kawai ta fita ta kada kuri'a ranar zaben gwamna a jihar Ekiti.

Folasade, mai shekaru 32, ta shaidawa kotun haka ne a takardar neman raba aurenta da mijinta, Gbenga.

"Ya zarge ni da barin yara a gida. Ya lakada min duka tare da caka min kwalba a hannu," inji Folasade.

Mijina ya lakada min na jaki don kawai na fita yin zabe - Wata mata ta sanar da kotu
Mijina ya lakada min na jaki don kawai na fita yin zabe - Wata mata ta sanar da kotu

Folasade ta ce haka ma mijinta Gbenga ke jibgar ta duk lokacin da ya kwankwadi barasa ya gudu. Kazalika ta shaidawa kotu cewar tuni ta hada kayanta ta bar gidan Gbenga.

DUBA WANNAN: Sun yi taron dangi sun kashe babbar soja, sun kone gawar ta

Folasade ta bukaci kotu da ta tursasa Gbenga biyanta 10,000 duk wata domin kulawa da yaransu guda biyu.

"Shekara 12 muna zaune tare duk da har yanzu bai biya kudin sadaki na ba. Ba ya daukan dawainiyar yaran da muka haifa," a cewar Folasade.

Bayan sauraron korafin Folasade, alkalin kotun, mai shari'a, Olayinka Akomolede, ta daga sauraron karar zuwa 28 ga watan Fabrairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng