Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda take kashe kudi kan fursunoni

Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda take kashe kudi kan fursunoni

- Akalla N15,000 kowanne fursuna ke ci a rana

- Akwai miliyoyin 'yan fursuna a kasar nan

- Wasunsu an ma manta da zamansu

Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda take kashe kudi kan fursunoni
Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda take kashe kudi kan fursunoni

A yanzu dai akwai miliyoyin 'yan Najeriya da ke zaune ko dai jiran hauni, mai rataya, ko jiran sharia, ko kuma zaman karas da kwanakinsu na hukunci da laifinsu ya gindaya, ko ma kawai zaman kansu domin gwamnati na so ta sakaya su saboda sun addabi al'umma.

Wasu 'yan fursunan ma dai, saboda tsabar sabo da zaman kurkuku, sun gwammaci su zauna a kurkukun ko bayan sun gama zaman kason nasu. Sukan gwammaci su sake aikata laifi domin su koma zaman cin abinci kyauta.

DUBA WANNAN: An hana kwastam bin shinkafa kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda kudin abinci da tsadar rayuwa ke mayar da ciyar da fursunoni wani babban nauyi. Inda takan kashe N15,000 kan kowanne dan kurkuku.

Wannan na nui dai, kowanne abinci da suka ci kudinsa Naira 5,000. To ko kudin abincin dare a Sheraton Hotel bai kai 5,000 a rana ba. A dai duba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng