Wani dan Najeriya ya sayi motar Commando Terminator na Amurka
- Wani dan Nakeriya ne mai arziki ya sayi hamshakiyar motar
- Obi Okeke, da aka fi sani da Dr Bugatti, ya sayi motar Mr Schwarzenegger kirar Bugatti Veyron a kan kudi dala miliyan biyu da dubu dari biyar
Mujallar Top Gear mai talla da bikin hamshakan motoci masu karfi da gudun tsiya, su suka wallafa labarin Mista Bugatti, wani dan Najeriya da ke iya kashe biliyoyi domin saye da sayar da motoci.
Obi Okeke, wanda aka fi sani da Dr Bugatti, ya sayi motar Mr Schwarzenegger kirar Bugatti Veyron a kan kudi dala miliyan biyu da dubu dari biyar, watai kusan naira biliyan daya fa kenan, a wannan zamani na Buhariyya da talauci.
Ita dai motar kirar Bugatti, a duniya sai hamshaqi ke iya sayenta, domin uwar tsadar da take da ita. An fi ganinta wurin 'yan kwallo da masu hannu da shuni, da a manyan fina-finai kamar su James Bond.
DUBA WANNAN: An hana kwastam bin shinkafa kasuwa
Shi dai Arnold, babban dan fim din Amurka, yayi suna a fina-finai irin su Commando, A-Team, Terminator, da ma Conan the Barbarian.
Haka zalika, ya rikide ya zama dan siyasa a jihar California wadda ya zo yana saurayi daga Turai, lokacin yana talakka futuk.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng