An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue

An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue

- Rundunar ‘yansadar Jihar Benuwe ta ce ta kama mutane da ake zargin su da kashe Fulani makiayya guda bakawai a ranar Laraba

- Rundunar 'yansadar jihar Benuwe ta dau alwashin daukar mataki mai tsanani kan duk wanda aka kama da hannu dumu dumu a wajen kashe Fulani

Rundunar ‘yansadar jihar Benuwe sun samu nasarar kama mutanen da ake zargi suna da hannu wajen kashe Fulani makiyaya guda bakawai tare da kona gawarwakin su.

A ranar Laraba ne wasu gungun mutane da ake zargin ‘yan Kabilar Tiv ne suka kashe Fulani makiyaya a garin Gboko.

A wata sanarwa da mai magana da yawun bakin rundunar ‘yansadar jihar Benuwe ya fitar, yace rundunar ta samu labarin aika-aikanne a a ranar Laraba da misalin karfe 9.30 na safe a tashar motar Gboko.

An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue
An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue

"An far ma makiyayan ne aka kashe su sannan kuma aka cinnawa gawarwakinsu wuta a tashar."

KU KARANTA : Hukumar EFCC ta zargi Suswam da yunkurin yaudarar mai ba da shaida akansa game da binciken da suke masa

Tuni gwamnan jihar Benuwe, Samule Ortom da kwamishinan ‘yansadar jihar, Fatai Owoseni, suka ziyarci wajen da abun yafaru dan ganewa idanun su.

Rundunar 'yansandan jihar Benuwe ta yi alkawarin daukar mataki mai tsanani akan duk wanda aka kama yana da hannu dumu-dumu wajen kashe Fulani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng