Taka leda: Najeriya ta doke kasar Sudan a gasar Afirka, ta tsallaka zuwa wasan karshe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sawun yan Najeriya wajen taya kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles biyo bayan lallasa kasar kungiyar kwallon kafa ta kasar Sudan ci 1-0 a gasar CHAN.
Kungiyar Super Eagles dake cike da yan wasan dake taka leda a gida Najeriya ta doki abokiyar karawarta ne a matakin na biyu da karshe, wanda ya bata daman shiga wasan karshe na gasar dake gudana a birnin Marrakesh na kasar Morocco.
KU KARANTA: Fusatattun Matasa sun hallaka ɓarawon Babur har lahira a Birnin Kebbi
Buhari ya nuna farin cikinsa da kokari tare da bajinta da yan wasan suka nuna, inda yace yana bin kadin nasarorin da kungiyar take samu tun daga farkon fara gasar, sa’annan ya yaba da kwarewar da yan wasan suka nuna, inda yace sun zamo abin koyi a nahiyar Afirka gaba daya.
Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina, wanda yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan wasan tare da masu horar dasu akan su jajirce don ganin sun zamo zakaru a gasar.
Daga karshe ya tabbatar musu da goyon bayah gwamnatinsa tare da goyon bayan yan Najeriya gaba daya a garesu don ganin sun lashe babban kyautar gasar a wasansu na karshe, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng