Ka gaji da bubbuge motarka? Ga wata mota da wani dalibin ABU ya ƙera wanda ba’a taɓa buga ta
Wani hazikin saurayi dake karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria a jihar Kaduna ya kera wata sabuwar mota, wanda babau yadda za’a yi ka buga ta, ko kuma ka yi hatsari a cikinta.
Legit.ng ta gano wannan motar ne a shafin kafar sadarwar zamani na Facebook, inda wannan dalibi mai basira yayi ma kansa lakabi da suna ‘Naija auto guru’, ma’ana fasihin mai kera motoci a Najeriya, kuma yace kera motar na daga cikin sharadin samun shaidar digirinsa a ABU.
KU KARANTA: Fusatattun Matasa sun hallaka ɓarawon Babur har lahira a Birnin Kebbi
Dalibin yace yana damuwa matuka game da matsalolin da ake yawan samu da motoci a Najeriya, musamman yawna hadduran motoci da ake samu akan titunan mu, don haka ya ci alwashin magance matsalar, musamman ganin cewa Najeriya ce ta dauki nauyin karatunsa na tsawon shekaru biyar.
Dalibin ya sanya ma motar tasa mai suna Leemah Mobil fasahar lura da kuma taka burki a duk lokacin da motar ta kusanci duk wani abu da za ta iya buga, ko kuma wanda zai janyo hatsari, haka zalika koda wata motar ko wani abu yayi kokarin bugunta ta baya, zata kara gudu da kanta, kuma ta kauce masa.
Ya cigaba da fadin ya kera motar ne duba da yawan haddura da ake samu, dake faruwa daga dukan mota ta gaba, ta gefe ko kuma ta baya, Inda yace tuni fasahar cin burkin ta yawaita a Duniya, inda ake sanya su a manya motocin alfarma, amma yace shi ya kirkiro fasahar kaucewar, shi ya fara daura shi a Mota.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng