Wasu malamai biyu na addinin Kirista sun riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsari na jihar Ondo
Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta cafke wani direban motar daukan kaya, Juwon Ariyibi, bisa laifin kisan mutane biyu da motarsa a garin Ipele na ƙaramar hukumar Owo ta jihar.
Kakakin hukumar, Mista Femi Joseph, shine tushen wannan rahoto da ya bayyana cewa, hatsarin ya afku ne a ranar Litinin din da gabata a yayin da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Fasto Oluwajuwon Adebayo da kuma Fasto Sunday Ajenifuja suke tafe a kan babur din su.
Legit.ng ta fahimci cewa, baya ga kasancewar su malaman addinin kirista sun kuma kasance malaman wata makarantar firamare ta gwamnati dake ƙaramar hukumar Akure ta Arewacin jihar, inda ajali ya yi musu halinsa a yayin da suke tafe a hanyarsu da zuwa wajen aiki.

Asali: Depositphotos
Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, an yi gaggawar miƙa wannan malamai biyu asibiti a yayin da hatsarin ya afku, wanda daga bisa ni suka ce ga garin ku nan.
KARANTA KUMA: Wani hamshaƙin ɗan kasuwa ya yi kuskuren kashe 'yar sa a jihar Imo
Kakakin hukumar ya ƙara da cewa, akwai tuƙin ganganci a ɓangaren direban babbar motar, kuma za miƙa shi kotu da zarar sun kammala bincike.
A na ta ɓangaren, shugabar cibiyar ilimi ta jihar Ondo, Misis Oladunni Odu ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da wannan tsautsayi da ya afkawa malaman, inda kuma ta miƙa saƙon ta'aziyartar ga iyalan wadanda suka yi rashin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng