Ina samun N150, 000 a kowane wata wajen sana'ar sayar da ƙosai
Wata bazawara da ba ta wuci shekaru 50 a duniya ba kuma uwar 'ya'ya huɗu, Fatima Abdullahi, ta yiwa rayuwar ta luɗufi wajen sana'ar sayar da ƙosai.
A madadin ta dirfafi barace-barace da 'yar murya wajen neman taimakon al'umma kamar yadda dattijai 'yan uwanta ke yi a wasu sassa na faɗin ƙasar nan, bazawarar ta dogara da kan ta inda take samun N5000 a kowace rana wajen sana'ar sayar da ƙosai da kuma koko.
Malama Fatima take cewa, ba ta buƙatar tallafin kuɗi a wurin gwamnati ko wata ma'aikatar kuɗi wajen fafutikar ta na samun nasara a rayuwar nan ta yanzu.
Wannan mata dai mai zuciyar neman na kan ta mazauniyar unguwar Rigasa ce ta ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, ta bayyana wa manema labarai a ranar larabar da ta gabata cewa, ta fara wannan sana'ar ne shekaru goma da suka gabata bayan rasuwar mijin ta.
Duk da cewar mijin ya rasu bai bar mata wani abin dogaro ba tare da 'ya'yayenta huɗu, hakan bai sanya ta lamunci sana'ar bara ba , inda ta yanke shawarar fara sana'ar sayar da ƙosai wanda a yanzu ta samu tabarraki mai tsoka a cikin ta.
Malama Fatima take cewa, "ta fara wannan sana'a ne da N3000, inda a sannu-sannu da hausawa kan ce sai dai a daɗe ba a je ba ta haɗa da sayar da dankalin hausa, kuma cikin yalwar tabarraki ta habaka domin kuwa a halin yanzu ta kan samu N5000 a kowace rana, kimanin N150,000 kenan a kowane wata."
Ta ci gaba da cewa, "duk da cewar akwai hatsari a sana'ar ta, kasancewar kullum ta na tsugunne bakin wuta, amma a hakan ta ke ɗaukar nauyin rayuwarta da kuma ta 'ya'yanta."
KARANTA KUMA: Rundunar sojin ƙasa ta shafe wani sansanin Boko Haram a dajin Sambisa
Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar The Punch cewa, wannan mata ta kirayi 'yan uwanta zaurawa har ma da waɗanda ke tare da mazajensu, akan su fara sana'a komai ƙanƙantar ta domin samun wadatar dogaro da kai.
Ta kuma bayyana rashin jin daɗin ta dangane da yadda wasu masu ƙarfi a jika ke kashe zukatansu wajen dirfafar sana'ar barace-barace, inda ta ƙara da cewa addinin musulunci yana fushi da wannan ɗabi'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng