Dalilai guda uku ƙwarara da suka sanya iyaye buƙatar haihuwar da Namiji fiye da Mace

Dalilai guda uku ƙwarara da suka sanya iyaye buƙatar haihuwar da Namiji fiye da Mace

Wani mummunan al’ada dake tashe a kasar Indiya shi ne zabar jinsin abin da ma’aurata ke bukatar Haifa, don gudun kauce ma haihuwar yaya mata, wanda a al’adar ake musu kallon marasa amfani.

BBC Hausa ta ruwaito a yanzu haka akwai sama da yan mata miliyan 21 a kasar Indiya, wanda iyayensu sun dai haifesu ne kawai ba tare da jin dadin haihuwarsu ba ko ganin amfaninsu ma gaba daya.

KU KARANTA: Fusatattun Matasa sun hallaka ɓarawon Babur har lahira a Birnin Kebbi Fusatattun Matasa sun hallaka ɓarawon Babur har lahira a Birnin Kebbi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin mutanen dake bin wannan al’ada suna yi ne wai don zubar da cikin haramun ne a wajensu, don haka sais u haife yar, kuma su yi watsi da ita, babban burinsu shi ne su samu da Namiji.

Dalilai guda uku ƙwarara da suka sanya iyaye buƙatar haihuwar da Namiji fiye da Mace
Yan matan Indiya

Bincike ya tabbatar da wasu dalilai guda uku da suka sanya ake kin haihuwa ya mace, aka fifita haihwua da namiji a kasar Indiya, da suka hada da: Gado, neman sadaki da kuma rabuwa da yayansu mata.

A al’adar Indiya, Namiji ne kadai ke jin gadon Iyayensa, ba’a baiwa mace ko allura, haka zalika a irin nasu al’adara iyayen Amarya ne ke biyan kudin aure da sadaki ba Ango ba, don haka kowa ke son a ce shi za’a biya sadaki, bugu da kari idan Miji ya mutu, matarsa komawa gidan iyayensa ta ke yi, don haka iyaye basu son rabuwa da yarsu.

Rahotanni sun bayyana an fi samun gudanar da wannan al’ada a garuruwan Punjab da Haryana, inda bincike ya tabbatar da ga duk yaro namiji guda daya akwai mata dubu 1 a garuruwan biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng