Hotunan taron majalisar ministoci da shugaba Buhari ya jagoranta a Yau
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu halartar taron majalisar zartarwa ta ranar Laraba 31 ga watan Janairu, wanda ya gudana a babban dakin taro dake fadar gwamnatin Najeriya.
Legit.ng ta gano ministoci da dama da suka halarci wannan zama na ranar Laraba, daga cikinsu akwai Ministan Ilimi Adamu Adamu, ministan ayyuka, lantarki da gidaje, Babatunde Fashola, minsitan sufuri, Amaechi, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da sauran ministocin Najeriya.
KU KARANTA: Fusatattun Matasa sun hallaka ɓarawon Babur har lahira a Birnin Kebbi

Haka zalika manyan jami’an gwamnati da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan Najeriya, Winnifred eyo Ita da kuma shugaban ma’aktana fadar shugaban kasa, Abba Kyari duk sun samu halartan zaman.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhar ya aike ma majalisun dokokin Najeriya, da suka hada da majalisar wakilai dakuma majalisar dattawa wata doguwar wasika inda yake bayyana musu matakan da gwamnatinsa ta dauka game da rikicin makiyaya da manoma.

Shugaban ya aika da wasikar ne biyo bayan tsegumi da ake yi a majalisun na cewa wai yayi watsi da mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon rikicin, inda wasu ma ke ganin wai don Fulani bane aka kashe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng