Sojojin ruwa sun yi ram da wasu 'yan sumogalin da suka shigo da kayyaki masu yawa ta barauniyar hanya

Sojojin ruwa sun yi ram da wasu 'yan sumogalin da suka shigo da kayyaki masu yawa ta barauniyar hanya

- Sojojin sun yi ram da wasu 'yan sumogalin da suka shigo da kayyaki masu yawa ta wata barauniyar hanya

- An kama 'yan sumogalin din ne a Ibaka, dake karkashin karamar hukumar Mbo a jihar Akwa Ibom

- Hukumar sojin ruwa ta mika su da kayayyakinsu ga hukumar kwastam domin zurfafa bincike da daukan matakin da ya dace

Jami'an hukumar sojin ruwa sun kama buhunhunan shinkafar kasar waje 759 da aka shigo da su Najeriya ta wata barauniyar hanyar ruwa dake Ibaka dake karkashin karamar hukumar Mbo a jihar Akwa Ibom.

Dakarun sojin sun kama wadanda ake zargi da shigo da shinkafar. Wadanda aka kama din su ne; Yahaya Balarabe; mai shekaru 32, dan jihar Borno, Godwin Owoyemi; mai shekaru 23 da Michael Aderemi, 'yan asalin jihar Ondo.

Sojojin ruwa sun yi ram da wasu 'yan sumogalin da suka shigo da kayyaki masu yawa ta barauniyar hanya
Buhunhunan shinkafa da dakarun sojin suka kama

Da yake magana da manema labarai a jiya, Kwamandan rundunar da suka kama 'yan sumogal din, Kaftin Yusif Idris, ya ce sun kama matasan ne yayin da suke shigo da kayan ta wata hanyar ruwa da misalin karfe uku na dare. Kazalika ya bayyana cewar sun mika su da dukkan kayan da suka same su da su ga hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam).

"Kamar yadda dokar hadin gwuiwar tsakanin hukumomin tsaron Najeriya ta tanada, hukumar sojin ruwa a wannan rana, ta mika wadanda jami'an mu suka kama da laifin sumogalin ga hukumar kwastam domin gudanar da bincike da daukan matakin da ya dace," a kalaman Kaftin Yusif.

DUBA WANNAN: Bulaliyar majalisa zai sha bulalar majalisa bisa kalamansa a kan gyaran jadawalin zabe

Kazalika, Yusif, ya gargadi masu sha'awar shigo da kaya ta barauniyar hanya, masu satar danyen man fetur, da kwacen jirgi da su canja tunani tun kafin su gamu da fushin dakarun sojin.

A jawabinsa, shugaban hukumar kwastam mai kula da ofishin hukumar na shiyyar gabas dake Fatakwal, Ajiya Masaya, ya ce yaki da al'amuran masu fasakwabri aiki ne dake da bukatar hada karfi wuri guda tsakanin hukumomin tsaro domin kare Najeriya.

Ya kara da cewar harkokin sumogalin na karya tattalin arziki, domin duk kasar da ta bar masu sumogalin su ci karensu babu babbaka, tabbas tattalin arzikin wannan kasa ba zai bunkasa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng