Bulaliyar majalisa zai sha bulalar majalisa bisa kalamansa a kan gyaran jadawalin zabe

Bulaliyar majalisa zai sha bulalar majalisa bisa kalamansa a kan gyaran jadawalin zabe

- Bulaliyar majalisar wakilai, Alasan Doguwa, ya bayyana cewar yunkurin majalisar wakilai na canja jadawalin zabe makarkashiya ce ga shugaba Buhari

- Kalaman Doguwa basu yiwa majalisar ta wakilai dadi ba

- Ana saka ran majalisar zata kakaba wa bulaliyar majalisar, Alasan Doguwa, takunkumi

A kwanakin baya ne Majalisar wakilai ta kasa ta yi gyare-gyare a jadawalin zabukan shekarar 2019 da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta fitar, inda ta mayar da zaben shugaban kasa ya koma karshe, sabanin a farko kamar yadda INEC ta fitar.

Bulaliyar majalisa zai sha bulalar majalisa bisa kalamansa a kan gyaran jadawalin zabe
Bulaliyar majalisa, Alasan Ado Doguwa

Saidai Bulaliyar majalisar ta wakilai, Alasan Ado Doguwa (dan jam'iyyar APC daga jihar Kano), ya ce bai amince da gyaran da majalisar tayi wa jadawalin gudanar da zaben ba. Doguwar ya bayyana yunkurin majalisar da cewar makarkashiya ce ga shugaba Buhari, a saboda haka shi ba ya tare da majalisar a kan wannan kudiri.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai ta fara yunkurin takawa bankuna birki a kan taba kudin masu ajiya

Kalaman na Doguwa basu yiwa mambobin majalisar dadi ba, musamman ganin cewar Doguwa na daya daga cikin shugabannin majalisar, a matsayinsa na bulaliyar majalisar wakilai.

Doguwa ya ja hankalin shugaba Buhari da kada ya saka hannu a kan dokar gyaran da majalisar ta yiwa jadawalin zabukan 2019 tunda dai dole sai ya amince gyaran zai zama doka.

Ana saka ran majalisar zata tattauna matakin da zata dauka a kan Doguwa yayin zamanta na yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng