2019: Shekarun Buhari ba za su hana shi kara tsayawa takara ba - Kungiyar FOGON

2019: Shekarun Buhari ba za su hana shi kara tsayawa takara ba - Kungiyar FOGON

- Muhammadu Buhari bai yin tsufan da zai hana shi kara tsayawa takara ba a karo na biyu a zaben 2019 inji kungiyar FOGON

Kungiyar FOGON ta ce kashi 50% na matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu Obasanjo ne ya janyo su

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu (FOGON) sun ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai yin tsufan da zai hana shi kara tsayawa takara ba a karo na biyu a zaben 2019.

Kungiyar ta yi kaca-kaca da tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, inda ta ce shine ummulaba’isin matsalolin duka matsalolin da kasa ke fuskanta a yanzu.

A wata sanarwa da kungiyar ta yi a taron manema labaru da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, ta ce Obasanjo bai isa ya faddawa al’ummar Najeriya abun da za su yi ba, ya bari mutane su ci moriyar dimokradiyya a zaben 2019.

2019 : Kashi 50% daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu Obasanjo ya janyo su
2019 : Kashi 50% daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu Obasanjo ya janyo su

Jagoran kungiyar, Wole Badmus, yace shugabaN Buhari mutumin kirki ne kuma yana da karfin da zai kara tsaya takara a zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

KU KARANTA : Ina aiki mai kyau a matsayina na shugaban ‘yansandan Najeriya - Ibrahm Idris Kpotun

“Babu yadda za a yi maganar lalacewar Najeriya ba ambato sunan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Kashi 50% daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu Obasanjo ne ya janyo su bayan haka, Badmus ya bayyana bakin cikin sa akan budadfiyar wasikar da Obasanjo ya rubuta yana kalubalanatar yananyin shugabancin Buhari

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng