Waiwaye: Mummunar rigimar da aka yi a Kano a 1953 wadda ta jawo asarar rayuka

Waiwaye: Mummunar rigimar da aka yi a Kano a 1953 wadda ta jawo asarar rayuka

- A tarihin dai 1953 ta zo wa da wasu da soyayyar neman 'yancin kai daga Turawan Ingila

- An kashe da dama a fadan da ya zama na kabilanci

- An shaffe kwanaki 4 ana tafka shi

Waiwaye: Mummunar rigimar da aka yi a Kano a 1953 wadda ta jawo asarar rayuka
Waiwaye: Mummunar rigimar da aka yi a Kano a 1953 wadda ta jawo asarar rayuka

Waiwayen mu na yau ya leka ne tarihi, inda muka dubo muku yadda rigimar kabilanci ta hargitsa jihar Kano har aka sami asarar rayuka da dukiyoyi da dama, a shekarun 1950s birnin mai tarihi.

An dai fara rigimar ne, kan ko ya dace a sami 'yancin kai, daga Turawa masu mulkin mallaka a wancan lokaci, ko kuma a'a, su dai jama'ar Arewa na ganin da saura, yankin nasu bai shirya ba, su kuwa na kudu, wadanda 'yan boko ne, ma'aikata, na gani lokaci ne na 'yanci ko ballewa.

DUBA WANNAN: Ya saki matarsa ya auro 'yar-tsana

An kwashe kwanaki hudu ana ta tafka ta'asa da kisa, da barna, wadda rigimar siyasa ce ta jawo ta. Samuel Akintola dai, yayi rangadin yakin kenan don yada akidar a nemi 'yanci, daga turawa, su kuma su Ahmadu Bello, suka ki goyon bayan wannan saboda yankin bai shirya ba,

An kai wa 'yan arewa a majalisar dokoki da ke Legas hari, saboda kokarin sai sun dakile kudurin da Antony Enahoro ke yi na sai an nemi 'yanci a shekarar 1954 su kuma na Arewa suka ce sai lokaci yayi.

Wannan shi ya jawo jama'a a Jihar Kano daukar barandami, adduna da qotoci, kamar dai na siyasar bana, suka fita suna kan mai uwa da wabi kan jama'a.

Samari ne daga Fagge, suka kai wa Sabon gari hari, da niyyar ci wa Yarabawa mutunci, bisa la'akari da Samuel Akintola na rangadi a yanki, sai dai kash, basu ma san waye baarabe ba, waye igbo, inda suka fi kashe kabilar Ibo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng