‘Yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a kasar

‘Yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a kasar

- Hukumar yaki da fataucin dan Adam da hadin gwiwar gwamnatin jihar Edo ta kaddamar da shirin tantance 'yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Libya

- ‘Yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a kasar

Faith Oboh, yarinya mai shekaru 22 tana cikin ‘yan gudun hijira 200 da suka dawo Najeriya daga kasar Libya wanda gwamnatin jihar Edo take tantance su a shirin da hukumar yaki da fataucin dan Adam ta shirya.

Masu tanatance mutane a wurin sun ga, Faith Oboh a cikin wani yanayin na ban tausayi.

A lokacin da take basu labarin ruyauwan ta a kasar Libya, Faith ta ce ita mai kitsu ne da gyaran gashin mata a Najeriya, amma tsananin talauci yasa ta yanke hukuncin tafiya kasar waje neman arziki.

‘Yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a kasar
‘Yan Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun bayyana irin bakar wahalar da suka sha a kasar

“Na dauki nauiyn tafiya ne da kudaden da na ta tara daga aikin kitsu da gyaran gashi mata da nake yi, sai da biya wata dillaliya naira N500,000 kafin na tafi kasar Libya.

KU KARANTA : Ina aiki mai kyau a matsayina na shugaban ‘yansandan Najeriya - Ibrahm Idris Kpotun

Burin na shine na shiga kasar Italiya ta tekun Libya, amma jirgin ruwan da muka shiga ya lalace mana akan hanya.

Sai da muka tsaya a cikin ruwa na tsawon sa’o’i 12 kafin matukin jirgin ya kira ‘yasandar Libya su zo su taimake mu.

“Daganan aka kai mu sansanin 'yan gudun hijira, inda na sha azaba na tsawon shekara daya da rabi da nayi a kasar.

”Yanzu da nake muku magana ban san inda dilaliyar da ta dauki nauyin tafiya na take ba, ban sani ba ko ta mutu ko tana raye.

Wata matashiya mai suna, Blessing Braimah, ,mai shekaru 34 da yara hudu ta ce tana kasuwancin sayar da kayan abincin ne Najeriya kafin ta karbi bashin N600,000 tafi kasar Libya neman arziki.

Wani matashi mai suna, Osaze Imafidon, yace rayuwar baza ta taba komawa daidai ba yayin da ya tafiya da sandar guragu.

Osaze Imafidon, yace an yanke mushi kafa ne bayan ya samu rauni ta sanadiyar harbin sa da aka yi da bindiga a sansanin da ake ajiye bakaken fata a kasar Libya.

Osaze, ya ce larabawan kasar Libya basa ganin bakaken fata da wani daraja, suna harbe su a duk lokacin da suka ga dama.

"Kuma inda suka siya sabin bindigogi akan bakaken fata suke gwadawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng