Darektoci a hukumar leken asiri ta kasa (NIA) sun bukaci a tsige sabon shugaban hukumar, sun bayyana dalilansu

Darektoci a hukumar leken asiri ta kasa (NIA) sun bukaci a tsige sabon shugaban hukumar, sun bayyana dalilansu

- Wasu darektoci a hukumar leken asiri ta kasa (NIA) sun nemi a canja sabon shugaban hukumar da Buhari ya nada kwanan nan

- Sun aike da kokensu a rubuce ga majalisun kasa domin neman goyon bayansu

- Sabon shugaban hukumar NIA na fuskantar zarge-zargen gaza cin jarrabawar karin girma da mallakar shaidar wata kasar bayan Najeriya

Wasu darektoci a hukumar leken asiri ta kasa (NIA) sun aike da takardar koke ga kwamitin majalisar wakilai a kan bukatar neman majalisar ta saka baki domin a canja sabon shugaban hukumar, Mista Ahmed Rufa'i Abubakar, da shugaba Buhari ya nada kwanakin baya.

A takardar da darektocin hukumar suka mika ga kwamitin majalisar ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, sun shaidawa majalisar cewar cire Mista Abubakar ya zama dole muddin ana son hukumar ta yi aikinta yadda ya kamata.

Darektoci a hukumar leken asiri ta kasa (NIA) sun bukaci a tsige sabon shugaban hukumar, sun bayyana dalilansu
Shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufa'i Abubakar

Da suke bayyana dalilansu a cikin takardar koken, darektocin, sun bayyana wa majalisar cewar wannan shine karo na farko a tarihin hukumar cikin shekaru 32 da aka taba nada wani mai mukamin kasa da darekta ya shugabance ta.

"Ya zama dole mu yi korafi saboda mutumin da aka nada ya shugabance mu, kasa yake da mu a aiki tun ma kafin a yi masa ritaya saboda ya gaza cin jarrabawar zama darekta," a cewar fusatattun darektocin.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai ta fara yunkurin takawa bankuna birki a kan taba kudin masu ajiya

Darektocin hukumar sun ce a shirye suke su fito da takardu da zasu tabbatar da faruwar hakan.

Kazalika sun bukaci majalisar wakilai ta binciki asalin kasar mista Abubakar ta haihuwa, domin, a cewar su, an haife shi ne a kasar Chadi, kuma a can ya yi wayo duk da yana ikirarin shi haifaffen Najeriya ne.

"Doka ta bukaci duk mutumin da za'a nada ya shugabanci hukumar sai an gudanar da binciken kwakwaf a kansa. A bayyane take cewar Mista Abubakar dan asalin kasar Chadi ne, kasar da ta dade tana takun saka da Najeriya. Muna tsoron zai iya mika sirrukan Najeriya ga abokiyar hamayyar ta, kasar Chadi," inji darektocin.

Darektocin da suka saka hannu a kan takardar koken sun hada da; EO Olanrewaju, Nelson Obiakor, da kuma Ahmed Sarki. Saidai majiyar mu ta ce sunayen da suka bayar ba ainihin sunayensu bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng