Jami'an tsaron kasar Kamaru 80 sun yi wa Najeriya kutse ta jihar Kuros Ribas

Jami'an tsaron kasar Kamaru 80 sun yi wa Najeriya kutse ta jihar Kuros Ribas

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa jami'an tsaron kasar Kamaru dake makwaftaka da Najeriya daga kudu su kimanin 80 ne suka yi wa kasar Najeriya kutse ta bakin iyakar ta da jihar Kuros Ribas.

Sai dai jami'an tsaron na kasar ta Kamaru da aka tambaye su dalili sai suka ce wai wasu tsagerun kasar ne suka biyo da suka tsallako ya zuwa Najeriya.

Jami'an tsaron kasar Kamaru 80 sun yi wa Najeriya kutse ta jihar Kuros Ribas
Jami'an tsaron kasar Kamaru 80 sun yi wa Najeriya kutse ta jihar Kuros Ribas

KU KARANTA: Za'a shimfida hanya zuwa dajin Sambisa

Legit.ng dai ta samu cewa akwai akalla 'yan kasar ta Kamaru akalla 5,000 dake gudun hijira a garin Danare dake a can jihar ta Kuros Ribas sakamakon wata 'yar hatsaniyar da aka samu a kasar ta Kamaru a watannin baya.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan Najeriya a karkashin inuwar wata jam'iyyar siyasa mai suna New Nigeria Nationalists a turance sun dunguma sun fara tattaki tun daga jihar Legas inda suka kuma nufi garin Abuja domin nuna adawar su ga salon mulkin shugabannin Najeriya.

Su dai wadannan mutanen sun bayyana cewa sun cika jikkunan su da guzuri sun kuma sha alwashin zuwa garin na Abuja a kasa domin nuna rashin jin dadin su game da yadda 'yan Najeriya ke shan bakar azaba kullu yaumin saboda rashin kyakkyawan shugabanci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng