Hukumar EFCC ta gargadi masu sayayya ta intanet kan danfara

Hukumar EFCC ta gargadi masu sayayya ta intanet kan danfara

- Ana satar kudaden mutane ta hanyar damfara a yanar gizo

- Mutane sun gwammace su yi sayayya da wayoyinsu a kawo musu har gida

- Hukumar EFCC ta ce wannan hanya sai an yi taka tsan-tsan

Hukumar EFCC ta gargadi masu sayayya ta intanet kan danfara
Hukumar EFCC ta gargadi masu sayayya ta intanet kan danfara

Sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a shafinta na yanar gizo a acebook a dazu da safe, tayi gargadi da jama'a su kula da satar 'yan danfara ta hanyar intanet da sunan ana sayayya.

Wannan na zuwa ne bayan da aka sami habakar yawan 'yan Najeriya masu harkar sayayya a yanar gizo, inda miliyoyin 'yan Najeriya ke kan yanar gizo a kullum.

Hukumar, ta sanar cewa, biyan kudaden da mutane kanyi kain a kawo musu kayan nasu na iya zama asara, muddin basu jira sunga kayan a kwar gidansu ba, don haka a daina biyan kudi sai kaya sun iso tukun, domin gudun 'yan damfara.

DUBA WANNAN: George Weah ya sanya wa kansa albashi

A yanzu dai, akalla 'yan Najeriya miliyan sittin 60m ne ke amfani da intanet a kullum, kuma da yawansu sukan yi sayayya ta shafukan sada zumunta, da wakilai irinsu jiji.com, konga da ma online shoppers dot com.

Wasu daga cikin irin wadannan ka iya zama na bogi, inda wasu kan yi amfani da su kawai don karbar kudin mutane su tsere.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng