Matar da ta gagari kamun 'yan sanda ta gamu da fushin kuliya

Matar da ta gagari kamun 'yan sanda ta gamu da fushin kuliya

- 'Yan sanda sun kama ta amma ta yi kukan kura ta kwace daga hannunsu

- Hukumar 'yan sanda ta ce matar mai suna joy ta yiwa jami'inta rauni

- Kotun Najeriya dake Kubwa a birnin tarayya ta yanke mata hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari

Wata kotu dake zamanta a yankin Kubwa dake birnin tarayya, Abuja, ta yankewa wata mata hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari.

Matar mai suna Joy, da ba'a iya sanin adireshinta ba, ta gurfana gaban kotun ne bisa tuhumar ta da laifin haikewa wani dan sanda tare da bijirewa kamu.

Joy ta amsa dukkan zargin da hukumar 'yan sanda ta gabatar gabatar kotu.

Matar da ta gagari kamun 'yan sanda ta gamu da fushin kuliya
Matar da ta gagari kamun 'yan sanda ta gamu da fushin kuliya

Da yake bayani a gaban kotun, dan sanda mai gabatar da kara, Babajide Olanipekun, ya shaidawa kotu cewar jami'an 'yan sanda sun samu Joy a gaban wani gidan rawa ranar 19 ga watan Janairu, kuma sun nemi ta yi bayanin kanta amma ta gaza yin hakan.

DUBA WANNAN: Saurayi da budurwar sun fada komar 'yan sanda bisa laifin jefar da dan gaba da fatiha

Olanipekun ya kara da cewar, Joy, ta yi tirjiya yayin da suka nemi tafiya da ita ofishinsu dake Kubwa.

Ya kara da cewar jami'an 'yan sanda sun kara yin kacibus da joy a ranar 20 ga wata, amma da suka kara kokarin kama ta sai tayi kukan kura ta yi kan jami'insu, Jide Ekundayo, har ta kai ga ta ji masa ciwo.

Da yake yanke hukunci, alkali kotun, Mohammed Marafa, ya bawa Joy zabin biyan tarar dubu takwas ko zaman gidan yari na watanni hudu, tare da gargadinta da ta zama mai hali nagari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng