Tabdijam: An samu shugaban kasa guda 2 biyo bayan rantsar da madugun yan adawa

Tabdijam: An samu shugaban kasa guda 2 biyo bayan rantsar da madugun yan adawa

Madugun yan adawa na kasar Kenya, Raila Odinga ya karbi rantsuwar zama shugaban kasar Kenya a gaban dubun dubatan masoya da magoya baya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Yan adawan sun yi hakan ne da nufin kalubalantar mulkin halastaccen shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, tare da nuna bacin rai da rashin amincewa da zaben da Kenyatta yayi ikirarin ya lashe.

KU KARANTA: Ana yi ma wata budurwa da ta musulunta a jihar Imo barazanar kasheta (Hotuna)

“Ni ne halastaccen shugaban kasar Kenyam babu wani da ke da ikon mulkin kasar Kenya da ya wuce ni.” Inji Raila Odinga.

Tabdijam: An samu shugaban kasa guda 2 biyo bayan rantsar da madugun yan adawa
Madugun yan adawa, Odinga

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da fari, Yansandan kasar sun yi kokarin tartwatsa taron magoya bayan Odinga ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa a cikin taron da suka shirya a tsakiyar babban birnin kasar, Nairobi.

Tabdijam: An samu shugaban kasa guda 2 biyo bayan rantsar da madugun yan adawa
Odinga da Uhuru

Idan za’a tuna, Odinga ya fadi ne a zanen shugaban kasar da ya gudana a ranar 8 ga watan Agustan shekarar data gabata, sai dai Kotun Koli ta kasar ta soke wannan zabe, inda ta bada umarnin a sake gudana da wani a ranar 25 ga watan Oktoba, amma Railan bai sake shiga zaben ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng