Saurayi da budurwar sun fada komar 'yan sanda bisa laifin jefar da dan gaba da fatiha

Saurayi da budurwar sun fada komar 'yan sanda bisa laifin jefar da dan gaba da fatiha

- An gurfanar da wata budurwa da saurayinta a gaban kotu bisa zarginsu da jefar da jariri

- Budurwar mai shekaru 15 da saurayinta, Abdullahi Isma'il, sun musanta tuhumar da ake yi masu

- Kotu ta mika jaririn hannun matar mai unguwa dake cikin jego domin samun kulawa

An gurfanar da wata budurwa, Hadiza, mai shekaru 15 da saurayinta, Abdullahi Isma'il, a gaban wata kotu a garin Jos, jihar Filato, saboda laifin jefar da wani jariri, a gefen hanya, da suka haifa babu aure.

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja Ahmed Labaran, ya shaidawa kotu cewar wani mutum ne mai suna Abdulkarim Danbadawai ya kawo korafin yasar da jaririn ofishin hukumar dake Angwan Rogo, a ranar 19 ga watan Janairu.

Saurayi da budurwar sun fada komar 'yan sanda bisa laifin jefar da dan gaba da fatiha
Saurayi da budurwar sun fada komar 'yan sanda bisa laifin jefar da dan gaba da fatiha

Saja Labaran ya kara da cewa, Danbadawai, ya kawo jaririn ofishin hukumar 'yan sanda tare da shaidawa kotu cewar yarinyar da ta haifi jaririn ta amsa cewar ta samu ciki ne bayan mu'amala da Abdullahi a wani Otal kwanar Chobe a garin Jos.

"Mahaifiyar Zainab tura ta Abuja, wurin 'yan uwanta, saboda gudun abin kunya, bayan ta gane yarinyar na dauke da juna biyu," inji Saja Labaran.

DUBA WANNAN: Naira biliyan N170.6 kudin tallafin man fetur muke bin gwamnati - NNPC

Bayan ta haihu ne ta dawo Jos ta nemi Abdullahi domin bashi jaririnsa. Bayan ya ki karbar jaririn ne da suka hadu ta ajiye shi a wurin kuma dukkaninsu suka tafi suka bar wurin.

"Nan suka bar jaririn yana kuka har Allah ya kawo Danbadawai, mutumin da ya kawo mana shi ofis," a cewar Saja Labaran.

Daga bisani mai shari'a ya damka jaririn a hannun matar mai unguwa dake cikin jego domin cigaba da kulawa da jaririn.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng