Manoma a Najeriya sun koka akan shi go da manja ta barauniyar hanya

Manoma a Najeriya sun koka akan shi go da manja ta barauniyar hanya

- Kungiyar manoman manja kwakwa sun yi kira da shugaba Buhari ya hana yawan shigo da manja da ake yi ta barauniyar hanya

- Shigo da manja daga ksashen waje barzanar ne ga tattalin arzikin Najeriya inji kungiya manoman manoman kwakwakn manja

Manoman kwakwaN manja a Najeriya dake karkakashin kungiyar ‘National Oil Palm Produce Association of Nigeria’ sun yi kira da shugaba Buhari, ya kawo karshen yawan shigo da manja cikin kasar da ake yi ta barauniyar hanya.

Manoman sun ce, manja daban-daban da ga kasashen waje suun cike kasuwanin Najeriya, wanda ‘yan kasuwa mara kishi ke shigo da su ta barauniyar hanya

Shugaban kungiyar na Jihar Ondo, Mista Biodun Adetula, ya ce shigo da manja da wa su ‘yan kasuwa ke yi ta barauniyar hanya, yana ma kasuwancin su zagon kasa.

Manoma a Najeriya sun koka akan shi go da manja ta barauniyar hanya
Manoma a Najeriya sun koka akan shi go da manja ta barauniyar hanya

A cewar Shugaban, a sakamakon wannan abin takaicin, farashin manjan sai faduwa yake ta yi tun daga watan Agusta na shekarar 2017, wanda hakan ya sabawa al’ada, a ce farashin manjan yana faduwa, maimakon ya tashi, a lokacin da ya kasance ba zamaninsa ba.

KU KARANTA : Fito da shugaban kasa daga yankin Ibo – Aisha Yusfu ta yi kaca-kaca da sakataren gwamnatin tarayya

A cewarsa, “Ko shakka ba bu, ana shigo da Manja ta wasu hanyoyin na daban cikin kasarnan, dukkanin kasashenmu na yammacin Afrika muna da kakar manjan daya ne da su.

Kuma hakan zai kara kashe tattalin arzikinmu, wanda ke samar da dubannin ayyukan yi ga matasanmu a wannan sashen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng