Najeriya: Fursunoni 430 sun samu shiga jami'a
- Hukumar kula da gidajen yari ta ba fursunoni 430 dama komawa jami'a yin karatu
- An yanke shawarar ba fursunoni shiga jami'a yin karatu ne dan inganta raywun su inji kakakin kula hukumar kula da gidajen yari
An bai wa fursunonin Najeriya 430 guraben digiri daban-daban a jam’ira (NOUN) dan inganta rayuwan su.
An kuma salami fursunoni 951 da da wasu masu ruwa da tsaki akan gayar gidajen yari suka tallafa musu.
A cikinsu akwai fursunoni uku da suke dab da kammala karatun digirinsu na uku a wasu jami'o'in Najeriya.
A cikin fursunonin akwai mutane uku da suke dab da kammala karatun digiri na uku a wasu jami’oi a Najeriya.
KU KARANTA : Fito da shugaban kasa daga yankin Ibo – Aisha Yusfu ta yi kaca-kaca da sakataren gwamnatin tarayya Read more: https://hausa.legit.ng/1149145-fito-da-shugaban-kasa-daga-yankin-ibo-aisha-yusfu-ta-yi-kaca-kaca-da-sakataren-gwamnatin-tarayya.html#1149145
An kyale fursunonin su ci gaba da karatun jami'a, a bangare na gyare-gyaren da gwamnatin Najeriya ke yi ga ayyukan shari'a, musamman ma na inganta rayuwar fursunoni.
Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya Mista Francis Enebore ne ya bayyana haka a birnin Abuja a lokacin da ya ke zantawa da manema labaru.
Mista Francis Enebore ya fadawa babban daraktan hukumar gyara ga gidajen yari na kasa, Dr. Uju Agomoh a wani taro da suka yi cewa sun salami fursunoni 951 bayan da suka cika dukkan ka'idojin da aka gindaya masu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng