An shirya wa ‘yan sara suka taron kara sanin juna a birnin Zariya

An shirya wa ‘yan sara suka taron kara sanin juna a birnin Zariya

- Makarantar Kitabu Wal-Sunnah ta shirya wa ‘yan sara-suka taron kara sanin juna a birnin Zariya

- Mallamai da 'yan siyasa sun gabatar wa sara sukan lacca akan illar shan miyagun kwayoyi

Makarantar Kitabu Wal-Sunnah dake layin sarkin Huda, Hayin Dogo Samaru dake karamar hukumar Sabon garin Zariya Kaduna ta shirya wa ‘yan sara-suka taron kara sanin juna da ‘yan siyasa ke amfani da su wajen bangar siyasa dan cimma burin su.

Makarantar ta gudanar da taron ne a ranar Asabar 28 ga watan Janairu da ya gabata.

Taron dai an gudanar da shi ne a babban masallacin juma’a dake bakin Dogo cikin garin Samaru, inda matasa daga bangarori da dama wanda galibinsu yan sara-suka ne na birni da kauye ciki da wajen garin na Samaru.

An shirya wa ‘yan sara suka taron kara sanin juna a birnin Zariya
An shirya wa ‘yan sara suka taron kara sanin juna a birnin Zariya

Malamai daga bangarori da dama suka halarci taron, wasu daga cikinsu sun gabatar da lacca masu ma’ana da amfani.

KU KARANTA : Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu

Sheik Musa Marhaba wanda yana daya cikin malaman, ya gabatar da lacca akan hukunce-hukuncen farauta a addinin musulunci, kuma yayi jawabi mai gamsar da matasa , masu mafarauta.

Bayan sauraren malamai wakilin Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Namadi Musa, darakta hukumar addinai ya gabatar da nasa jawabain a madadin gwamnatin jihar Kaduna.

Daraktan ya yi kira ga iyaye maza da mata da su kula da tarbiyar ‘ya’yansu a ko da yaushe, don kaucewa irin hadarin da ake ciki a wannan zamani na shan miyagun kwayoyi.

Ya ce, abin mamaki da takaici shi ne yadda lamarin ya shiga har cikin matan aure tsofaffi da matasan yan mata.

Daraektan ya ce, wannan bala’i ne babba kuma tuni gwamnatin jihar kaduna ta yi tsari na musamman don taimakawa irin wannan taro na son taimakon matasa tare da basu mafita ta gari da zata taimakamasu wajan samar da rayuwa mai tsafta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng