PDP ta bayyana damuwarta akan lambar yabo da kungiyar AU ta ba shugaba Buhari akan yaki da cin hanci da rashawa
- Kungiyar gamayyar kasashen nahiyar Afrika ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari lambar yabo akan yaki da cin hanci da rashawa
- Babban jam'iyyar adawa na Najeriya ta yiwa shugaba Buhari ba'a akan lamabar yabo da kungiyar AU ta bashi
Jam’iyyar PDP ta ce lambar yabo da aka ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin jagoran yaki da cin hancin da rashawa a nahiyar Afrika abun mamakin ne da ban dariya.
A jawabin da sakataren jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yayi a ranar Litinin 29 ga watan Janairu, ya ce lambar yabo da kungiyar gamayyar kasshen nahiyar Afrika (AU) ta ba shugaba Buhari abun dariya ne da ban mamaki, saboda basu irin cin hanci da rashawa dake gudana a karkashin gwamnatin Buhari ba.
Ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da lamabar yabon da kungiyar AU ta ba Buhari wajen daga daraja da kimar sa da ya ragu a idanun mutane.
KU KARANTA : Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu
Jam’iyyar PDP ta ce, inda kungiyar AU ta san irin cin mutunci da Buhari yake yiwa mambobin jam’iyyar adawa da sunan yake da cin hanci da rashawa da baza taba bashi lamabar yabo ba.
PDP ta ce mutumin da ake ba lamabar yabo akan cin hanci da rashawa ya kasa yiwa al’ummar Najeriya bayyani aka bakadalar kwangilar naira triliyan daya da kamfanin NNPC ta ba da, ba tare da bin kai’da ba, da wani ministan sa ya tona a budadiyar wasikar da ya rubuta masa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng