EFCC ta damke dan takarar Gwamna na 2019 a jihar Gombe
Rahotanni sun kawo cewa a safiyar Litinin 29 ga watan Janairu, hukumar EFCC ta damke dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a 2019 a jihar Gombe, Alhaji Bala Bello Tinka.
Tinka ya kasance na kusa da Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya kuma kasance daga cikin manyan masu neman takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP.
Wani babban majiyi a hukumar EFCC ya bayyana cewa hukumar ta tafi da shi ne a ranar Laraba na mako da ya gabata don cigaba da bincike bisa zargin kasancewar shi da hannu a badakalar kudaden yakin neman zabe a 2015.
Bala Tinka, wanda ya kasance babban manajan kamfanin Tinka Point Construction ya kasance a hannun hukumar EFCC fiye da sa’o’i 24.
KU KARANTA KUMA: Duniyar bakin mutum tana bukatar mutanen Najeriya domin ta cigaba - Aregbesola
Majiyin EFCC ya bayyana cewa karo na biyu kenan da hukumar ke damkar shi a ofishinta na Gombe bisa zargin kasancewa da hannu cikin rabe-raben kudin yakin neman zabe don neman nasara ga jam’iyya mai mulki a lokacin zaben kasa a 2015.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng