Yan siyasa na yawan karerayi domin samun mulki - Yakubu Dogara

Yan siyasa na yawan karerayi domin samun mulki - Yakubu Dogara

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Hon Yakubu Dogara, ya caccaki jam'iyyun siyasa masu shilla karerayi wa jama'a domin cin zabe.

Dogara ya yi wannan jawabi ne jiya Litinin, 29 ga watan Junairu, 2018 a Abuja wajen taron da cibiyar shugabannin jam'iyyun siyasa ta shirya.

Game da cewarsa, zalunci ne ga kowani gwamnati ta hau ragamar mulki amma ta ki aiwatar da manufan jam'iyyarta.

KU KARANTA: Dangote ya gina makarantan kasuwanci na kimanin N1.2bn ma jami’ar Bayero

Yace: "Ya zama wajibi in ambaci cewa da dama daga cikin jam'iyyun siyasa sun ka yi alkawuran da suka san ba zasu iya cikawa ba domin hawa ragamar mulki. cuta ne a siyasa wata gwamnatin da aka zaba tayi watsi da manufar da aka bayyanawa jama'a kafin zabe.

Wajibi ne jam'iyyun siyasa su tabbatar da cewa manufarsu ya zama abubuwan da zai kawo cigaba ga kasa ga baki daya."

Yan siyasa na yawan karerayi domin samun mulki - Yakubu Dogara
Yan siyasa na yawan karerayi domin samun mulki - Yakubu Dogara

Zaku tuna cewa jam'iyyar adawa ta PDP da masu sharhi sun bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar APC bata cika alkawarin garambawul da yiwa mutanen Najeriya kafin zaben 2015 ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng