Yaron mota ya fado daga mota, ya rasa rayuwarsa
Wani direban mota dan shekara 25, John Okoye, ya yi tukin gangancin wanda yayi sanadiyar fadowan yaron motarsa daga cikin mota har ya rasa ranasa.
John Okoye wanda mazaunin Adensin Street, Igando, ya gurfana a gaban kotun majistaren Ojo da ke cikin garin Legas da laifin kisan kai.
Lauyan hukumar yan sanda, Insp. Uche Simeon, ya bayyanawa kotu cewa direban ya aikata wannan laifi ne ranan 17 ga watan Afrilun 2017 misalin karfe 8 na dare a hanyan Iyana-Iba/Igando, Ojo Lagos.

Lauyan yace: “Yaron motan mai suna Matthias Nwoge, ya fado daga cikin mota yayinda direban ke tukin ganganci saboda saurin daukan fasinja.”
“A kai Nwoge asibiti inda aka tabbatar da mutuwansa,”
KU KARANTA: Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu
Alkalin kotun, Mr A. A. Adesanya, ya bada belin N200,000 da mutane 2 da zasu tsaya masa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng