Ana yi ma wata budurwa da ta musulunta a jihar Imo barazanar kasheta (Hotuna)
Wata budurwa mai suna Aisha Obi, da ta Musulunta a shekarar da ta gabata a garin Owerri na jihar Imo ta fara samun barazana ga rayuwarta daga wasu mutanen kabilarta.
Legit.ng ta ruwaito Aisha Obi ta bayyana wannan barazana ga rayuwarta ne a shafin ta na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda mutumin dake mata barazana mai suna ‘Riverman Biafra Solder’ yace zai kashe ta matukar ta kai musulunci kasar inyamurai.
KU KARANTA: An caka masa: Tsohon dan majalisa ya maka Amaryarsa tare da ‘Mai dalilin aure’ gaban Kotu
“Ina fata zaki tsaya da addininki a Arewa, dan idan ki ka sake ki ka kawo shi nan, toh kin mutu kawai, ina so ki fahimci ba da wasa nake ba, kuma mu inyamurai ba zamu karbi addinin Almajirai ba, don haka kada ki shigo yankin mu, ko kuma rayuwarki ta shiga hadari.” Inji shi.
Sai dai a nata ra’ayin, Aisha ta ce wanda ya aiko mata da wannan barazana ba shi da aiki, “Amma ina fata ya Musulunta, kuma ma bai san cewa addinin Musulunci ya dade a kasar Inyamurai bane.” Inji Aisha.
Daga karshe Aisha ta ja kunnen mutumin da kada ya sake ya roke ta afuwa idan yaga jami’an tsaro sun fara nemansa ruwa a jallo, don kuwa kowa na da damar yin addinin da yake so a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng