Iyalan hadimin Gwamna Shettima da ya rasu zasu dunga karban alawus na N11m duk wata

Iyalan hadimin Gwamna Shettima da ya rasu zasu dunga karban alawus na N11m duk wata

Iyalan marigayi hadimin Gwamna Kashim Shettima, Muhammed Azare, sun samu gudunmawar kimanin naira miliyan 11 daga jami’an gwamnati, a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu.

Gwamna Shettima ne ya kafa asusun taimakon domin tallafawa iyalan Mista Azare, wanda ya rasu a makon da ya gabata bayan dan gajeren rashin lafiya.

Iyalan nasa wanda suka hada da mata biyu da yara, zasu kuma fara cin amfanin alawus na wata-wata daga gwamnatin jihar Borno.

Mista Shettima ya bayyana marigayi Azare, Inspekta na yan sanda a matsayin bawan Allah wanda ba’a taba samunsa da aikata wani laifi ba tunda ya fara masa aiki daga 2011.

Iyalan hadimin Gwamna Shettima da ya rasu zasu dunga karban alawus na N11m duk wata
Marigayi Muhammed Azare

A wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Mista Isa Gusau ya nuna cewa kudaden da aka tattara ya hada da naira miliyan 5 daga Gwamna Shettima, naira miliyan daya daga mataimakin gwamna, Usman Durkwa, naira miliyan biyu daga kwamishinoni da kuma naira miliyan 2.7 daga yan majalisun jiha wadanda suka harhada naira 1,00,000 ko wannensu.

KU KARANTA KUMA: Buhari na da niyan barin mulki – El-Rufai

Ana sanya ran Karin taimako daga majalisar dokoki.

Mista Gusau ya ce za’a kafa kwamitin mutane uku da zasu dunga kula da ilimin yaran marigayin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng