Ina da tabbacin APC zata yi nasara a zaben shugabancin kasa, zamu kawo jihohi 24 a 2019 – Inji El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bada tabbacin cewa jam’iyyarshi, APC, zata yi nasara a zaben shugabanci kasa sannan kuma zata riko jihohinta 24 a 2019.
Gwamnan ya fadi haka ne a wani hira da yayi a shirin gidan talbijin na Channels a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu.
“Bana shakka har a zuciyana cewa zamu yi nasara a zabuka masu zuwa ba a tsakiya ba kadai amman zamu gabatar da jihohinmu 24, ko fiye da haka.” inji shi
Tattare da caccaka da ake kai ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanan nan, El-Rufai ya yarda cewa APC zata ci gaba da kasancewa mai mayar da hankali akan sauke alkauranta na yakin neman zabe ga yan Najeriya.
Ya ce Najeriya ta rabu biyu, inda yake jaddada cewa rashin amincewa yana zuwa ne daga zababbun kungiyar mutane yayinda gwamnatin Tarayya take sane da ra’ayin mutane.
Yayinda yake nuna ra’ayinsa game da jawabin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gabatar a ranar Talata a makon da ya gabata, Gwamna El-Rufai ya ce bai karanta ba tukun, inda ya lura cewa “baya da lokacin karanta jawabi mai tsawo.”
KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku ne kadai ya zamo dodon jam’iyyar APC – Jigon PDP
Ya ce gwamnatin Buhari bata damu ba akan jawabin kamar yanda fadar shugaban kasa da jam’iyyar suka mayar da martini akan al’amura da tsohon shugaban kasan yayi tsakaci akai.
A cikin wasa gwamnan ya ce ya kasance mai biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma zai cigaba da hakan har illa masha Allahu.
Duk da haka, ya ce kasancewarshi daga cikin wadanda ke bukatar shugaban kasar sake tsayawa takara bai don cin amfanin kanshi bane alla ra’ayin mutane.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng