Dandalin Kannywood: Tsohuwar jaruma Abida Muhammad ta sake aure na 2
- Tsohuwar jaruma Abida Muhammad ta sake aure na 2
- Jrumar ta sake aure ne a ranar 26 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki
- Jrumar ta auri masoyin ta ne mai suna Al-Mustapha Abubakar akan sadaki Naira dubu 100
Labarin da muke samu sun tabbatar mana da cewa tsohuwar fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta sake zama amarya a karo na biyu a rayuwar ta.
KU KARANTA: An bankado kasuwar jarirai a garin Abuja
Mun samu dai cewa jarumar ta sake aure ne a ranar 26 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki biyo bayan rasuwar mijin ta da suka kasance a tare na tsawon shekaru mai suna Marigayi Hamza Danzaki.
Legit.ng haka zalika ta samu cewa jarumar ta auri masoyin ta ne mai suna Al-Mustapha Abubakar akan sadaki Naira dubu 100 da aka biya nan take da kuma aka gudanar a garin Kano.
Fitacciyar jarumar dai ta yi tashe sosai a masana'antar shirya fina-finan na Hausa a shekarun baya inda ake kallon ta a matsayin daya daga cikin fitattun jaruman da suke da kwarewa musamman ma wajen rawa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng