Hotunan Buhari yayin da yake kallon yadda kungiyar kwallon Najeriya ta lallasa kasar Angola

Hotunan Buhari yayin da yake kallon yadda kungiyar kwallon Najeriya ta lallasa kasar Angola

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalli wasan Najeriya

- Kungiyar Super Eagles ta lallasa kasar Angola 2-1

Hausa sun ce rai dangin goro, kuma hakan ne ya tabbata a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin tafiyar da yayi zuwa kasar Habasha inda ya halarci taron kungiyar kasashen Afirka.

An fara wannan taro ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, inda aka kwashe awanni ana tattauna batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka. Bayan dawowar Buhari masaukinsa a gida ne, sai aka hange shi ya kunna talabijin don kallon wasan Najeriya da kasar Angola a gasar CHAN.

KU KARANTA: Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna

Hotunan Buhari yayin da yake kallon yadda kungiyar kwallon Najeriya ta lallasa kasar Angola
Buhari

A yayin wannan fafatawar da ta gudana tsakanin Super Eagles da kungiyar kwallon kafa na kasar Angola, Najeriya ta samu nasara a kan Angola, inda ta lallasa ta 2-1, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hotunan Buhari yayin da yake kallon yadda kungiyar kwallon Najeriya ta lallasa kasar Angola
Buhari

Da wannan ne Najeriya ta samu tsallakawa zuwa zagaye na uku da karshen gasar. Wannane ne karo na biyu da shugaban kasa ke kallon wasan kungiyar Super Eagles, inda a yayin wasannin neman gurbin zuwa gasar kwallon kafa ta Duniya ma aka hange shi yana kallonsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng