Jami'an 'yan sanda sun damke wasu 'yan fashi kafin su tafka wata mummunar barna
- Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya sun yi nasarar cafke wasu 'yan fashi da makami kafin su aikata mummunar sana'ar su
- An cafke 'yan fashin ne yayin da suke tsaka da kokarin fara tare wata babbar hanyar ababen hawa
- An mayar da binciken 'yan fashin sashen hana aikata miyagun laifuka na hukumar 'yan sanda
Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun sun tabbatar da damke wasu 'yan fashi guda biyu a garin Kara dake daf wata gada a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan yayin da suke shirin fara tare hanyar domin fashi ga masu ababen hawa.
Legit.ng ta samu rahoton cewar kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya sanyawa hannu kuma ya mika ta ga jaridar Tribune Metro.
Jami'in hukumar yansanda mai kula da ofishinsu dake redemption camp, SP Olaiya Martins, ya bayar da umarni ga jami'an da suka kama 'yan fashin. Wadanda aka kama din sune; Jimoh Ganiyu; mai shekaru 22, da Al-Amin Oyindamola.
Matasan biyu sun dade suna aikata fashi kafin su fada komar hukumar 'yan sanda a yau.
DUBA WANNAN: Hotunan Gwamna da jami'an gwamnatinsa yayin atisaye a kan Kekuna
Oyeyemi ya ce sun kama wata bindigar gida da alburusai a wurin 'yan fashin bayan wata waya kirar Tecno da kuma wata jakar sabbin kayan sakawa.
Tuni aka mika su hannun jami'an SARS domin zurfafa bincike bisa umarnin kwamishinan 'yan sanda a jihar, CP Ahmed Iliyasu.
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, mataimakin shugaban hukumar 'yan sanda ya tabbatar da cewar jami'an hukumar sun yi nasarar tserar da wasu 'yan kasar Afrika ta Kudu su biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna. Kwamandan da ya jagoranci aikin kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su, Abba Kyari, ya tabbatar da kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng