Taron AU: An zabi shugaba Buhari ya zama jagoran yakar cin hanci a nahiyar
- Mahalarta taron AU na Habasha, sun zabi shugaba Buhari a matsayin uban yaki da rashawa
- A taron da yake gudana a gabashin Afirka
- An kiyasta kudaden da aka sace daga nahiyar a tiriliyoyi
Shuwagabannin kasashen nahiyar Afirka sun yi mubayi'a, sun sarawa shugaban Najeriya Alhaji Muhammadu Buhari, kan yaki da cin hanci da yake yi a kasarsa tun bayan da ya karbi mulki.
Shugaba Buhari a jawabinsa, ya zayyana irin gagarumin ci gaban da kasar sa ta samu kan yaki da tsiyayar kudaden talakawa zuwa aljihwan masu siyasa.
A tawagar da ya je da ita dai, harda tsofin shugaba Obasanjo da Abdussalami Abubakar, sai kuma ministocin tsaro da cikin gida, da ma kuma Ibrahim Magu, dansanda mai shugabantar EFCC na wucin gadi.
DUBA WANNAN: In Buhari ya dage zamu yaga APC
An dai zabi shugaba Buhari a matsayin jarumin jagora na yaki da rashawa a nahiyar baki daya a taron a yau, matsayi wanda zai rike shekara guda.
Afirka dai na cikin talauci, kuma satar kudaden gwamnati na ta kara kassarar da dan abin hannun da kasashen yanki ke jalantaawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng