Kotu ta umurci wani babba sojan ruwa mai ritaya ya biya wani makiyayi diyyar Naira miliyan N9m ta dalilin tsare masa shanu 42
- Kotu ta umarci Vice-Admiral Samuel Olajide Afolayan mai ritaya ya biya wani makiyayi diyyar Naira miliyan N9m akan kwace mi shi shanu 42 da yayi
- Samuel Olajide Afolayan zai rika biyan N500,00 a kowani wata har sai ya kammala biyan duka kudaden da kotu yanke masa hukunci ya biya akan laifin tsare ma makiyayi shanu
Kotun koli na Ilorin ta umarci, wani babban tsohon sojan ruwa, Vice-Admiral Samuel Olajide Afolayan mai ritaya, ya biya wani makiyayi mai suna, Alhaji Abubakar Abdullahi, diyyar naira miliyan N9m saboda tsare masa shanu 42 da yayi ba a bisa ka’ida ba.
Alkalin kotun, Jastis Adeyinka Sikiru Oyinloye, ya umarci sojan ya rika biyan makiyayin, N500,000 a kowani wata har ya kammala biyan duka kudaden da kotu yanke masa hukunci ya biya.
Makiyayin, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya ce kwace masa shanu guda 60 da sojan yayi rashin adalci da karya doka.
Kuma ya bukaci soja ya gaggauta sakar masa shanun sa, kuma ya fito fili ya nemi gafarrar sa a kafafen watsa labaru a cikin nan da makonni biyu.
KU KARANTA : Iyabo Obasanjo ta yi magana akan wasikar da mahaifinta ya aikawa Buhari
Afolayan ya fada ma kotu cewa, makiyayin ya shiga cikin gonarsa da shanun sa, inda suka masa barnar shukar roga da masara da yayi, wanda farashin su ya kai kimanin naira miliyan N2.5m bayan haka makiyayin ya kona masa gonar sa.
A lokacin da Jastis Oyinloye, yake gudanar da shariar, makiyayin yayi ikrarin cewa shanu 60 aka kwace masa, amma shi sojan yace shanu guda 42 kacal ya kwace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng