Kotu ta dakatar da hukuncin ratayar wani makashi, bayan da yace ya manta laifin da ya aikata

Kotu ta dakatar da hukuncin ratayar wani makashi, bayan da yace ya manta laifin da ya aikata

- An zartas ta hukuncin kisa a kansa tun 1980s, saboda kisan dan-sanda

- Ya shafe shekaru 30 yana jiran a kashe shi, sai dai har ya tsufa

- Rashin lafiya ta kama shi, da cutar mantuwa, alkali ya dakatar da a kashe shi

Kotu ta dakatar da hukuncin ratayar wani makashi, bayan da yace ya manta laifin da ya aikata
Kotu ta dakatar da hukuncin ratayar wani makashi, bayan da yace ya manta laifin da ya aikata

A can kasar Amurka, an sami wani dattijo dan shekara 67, wanda yana daga cikin masu laifi mafi dadewa a jerin deathrow, watau masu jiran hauni, da cutar mantuwa.

A shekarun 1980s ne dai ya aikata kisan kai, inda ya kashe wani dansanda, kuma alkalin kotu ya same shi da laifi, sai dai bayan shekaru 30, ya sami harbin zuciya da ma cutar mantuwa a kwakwalwa.

Sai dai bayan da lokacin kashe shi yazo a ranar alhamis da ta gabata, sai yace shi baisan me yayi ba za'a kashe shi, yayi ta runto da kururuwa, dole tasa lauyansa ya garzaya gaban alkali domin samun sabuwar oda.

DUBA WANNAN: Boko Haram na kara karfi

A sau uku dai ana daga kara ana samunsa da laifin kisan na 1985, kuma har kotun koli an je. Sai dai kotun ce yanzu ta dage kisan nasa ta hanyar allurar mutuwa.

Lauyansa ya ce ya tsufa kuma bashi da kwari, ba zai iya fuskantar hauni ba, ba kuma zai iya tuna me yayi wa jama'a ba, don haka a yi masa afuka da sassauci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng