Hotunan Gwamna da jami'an gwamnatinsa yayin atisaye a kan Kekuna
- Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, da mataimakinsa, Rt. Honarabul Ude Oko Chukwu, sun yi rangadin babban birnin jihar, Umuahia, a kan kekuna
- Wannan lamari ya jawo hankulan jama'a a dandalin sada zumunta, musamman ganin yadda shugabanni ke fargabar fitowa cikin jama'a ba tare da tsaro ba
- Jama'a na gannin gwamnan ya burge su domin wasu gwamnonin ko da wasa ba zasu iya fara gwada hakan ba
Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, mataimakinsa, Rt. Honarabul Ude Oko Chukwu, da wasu manyan Jami'an gwamnatin jihar, sun yi rangadin babban birnin jihar, Umuahia, da safiyar ranar Juma'a.
Wannan lamari ya jawo hankulan jama'a a dandalin sada zumunta, musamman ganin yadda shugabanni ke fargabar fitowa cikin jama'a ba tare da cincinrindon motoci ba da dandazon jami'an tsaro.
DUBA WANNAN: Sanatan PDP da magoya bayansa fiye da dubu goma sun koma jam'iyyar APC a jihar Kano
Jama'a na gannin gwamnan ya burge su domin wasu gwamnonin ko da wasa ba zasu iya fara gwada irin wannan abu da gwamna Ikpeazu ya yi ba saboda tsoron abinda hakan iya haifarwa tsakaninsu da jama'ar da su ka zabe su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng