Koriya ta Arewa ta fara shirin yaƙin duniya na uku

Koriya ta Arewa ta fara shirin yaƙin duniya na uku

Rahotanni da sanadin shafin mujallar TRT Hausa sun bayyana cewa, ƙasar Koriya ta Arewa ta ci gaba da jefa firgici tare da razani a zukatar shugabannin ƙasashen Yammacin Duniya, inda a halin yanzu suka ankara da cewa, tuni ta fara gudanar da shirye-shiryen yaƙin duniya na uku.

Mujallar ta kuma ruwaito cewa, shugaban ƙasar, Kim Jong Un ya bai wa ilahirin ma'aikatan ƙasar hutun mai tsayin gaske, domin kowa ya noma isasshe tare da yin guzurin abinci da zai wadatar da ƙasar a yayin da ake fafatawa a filin yaƙi.

Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un

Legit.ng ta fahimci cewa, al'ummar ƙasar sun duƙufa tuburan wajen bin umarnin shugaban ƙasar na su, inda kowanen su ya daura damarar fuskantar duk wani ƙalubale da zai tunkaresu.

KARANTA KUMA: Almundahanar N11bn: Kotun ƙoli ta umarci Shema ya fuskanci shari'a

Shugabannin kasar sun tabbatar wa duniya, shirye suke a wajen fafata yaki da kuma yin fito-na-fito da duk wata kasar da ke ji da kanta.

A halin yanzu dai, shugaba Kim Jong Un, ya gargadi dukkanin ƙasashen duniya masu ji da kansu da cewar ƙasar sa tana cikin shirin yin fito na fito domin fafatawa a yaƙin duniya na uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel