Yadda ake sa rai zata kaya tsakanin Obasanjo, Atiku da Kwankwaso da Buhari a 2019

Yadda ake sa rai zata kaya tsakanin Obasanjo, Atiku da Kwankwaso da Buhari a 2019

- Kwankwaso zai iya kara wa da Buhari a cikin APC a zaben cikin gida

- Ana sa rai zasu kafa wata jam'iyyar muddin ya sha kaye a hannun shugaba Buhari

- Atiku zai fuskanci masu adawa a cikin gida na sabuwar Amaryarsa kuma tsohuwar matarsa jam'iyyar PDP

Yadda ake sa rai zata kaya tsakanin Obasanjo, Atiku da Kwankwaso da Buhari a 2019
Yadda ake sa rai zata kaya tsakanin Obasanjo, Atiku da Kwankwaso da Buhari a 2019

Masu sharhin siyasa sun fara lissafin yadda zata kaya a zabukan da za'a shiga a badi a matakin shugabancin kasa, wanda ya dauki sabon salo a makon nan bayan da tsohon shugaba Obasanjo ya rubuta wa shugaba Buhari cewa baya tare da shi a 2019.

A 2003, da 2007 da 2011 dama dai janar da janar din basu ga-maciji da juna, inda aka sha gwa-gwagwa da jam'iyya mai mulki ta PDP da Muhammadu Buhari a jam'iyyu da suka tsayar da shi takara.

Sai dai hakan ta canja bayan da suka sami fahimtar juna a 2014, bayan karfin ta'addanci na Boko Haram, da ma wasu gwamnonin PDP da suka yaga jam'iyyar suka koma sabuwar jam'iyya hadakar masu adawa da mulkin PDP.

DUBA WANNAN: Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajirci

Babu alama dai cewa shugaba Buhari zai hakura da mulkin, muddin dai yaga lafiyarsa ta dore da inganta. Haka zalika, masu adawar cikin gida, irin su Bukola Saraki, gwamnoni irin su Abdulfattah Ahmed na Kwara, da ma watakila Bindow na Adamawa.

A hangen masu fashin bakin dai, za'a iya ganin sun kafa sabuwar jam'iyya muddin PDP ta tsayar da Atiku Abubakar, wanda dama ba shiri suke da Obasanjo ba, a wani shiri da aka ji suna kira 3rd option, watau zabi na uku.

Idan babban zaben ya zo ka kasa samun wanda yayi ice cikin mutum iye da biyu, wannan na nufin sai an je zagaye na biyu kenan domin idda gwani.

Wadanda ake gani zasu kai labari su kuma yi rawar ganii sun hada da Bukola Saraki na Kwara, Tinubu na Lagos, Shugaba Buhari, Sule Lamido, Rabiu Kwankwaso, da Alhaji Atiku Abubakar, Wadannan sune ake sa rai zasu iya nuna sha'awar takara a badin, ko a cikin gida ko a babban zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng