Nigerian news All categories All tags
Addinin Allah: Musuluntar shugaban jam'iyyar makiya Islama ta firgita duniya

Addinin Allah: Musuluntar shugaban jam'iyyar makiya Islama ta firgita duniya

Ko shakka babu hankulan mutane masu matukar kiyayya ga addinin islama sun yi matukar kaduwa tun bayan lokacin da daya daga cikin manyan shugabanninsu ya furta kalmar shahada tare da rungumar addinin a kasar Jamus.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a makon da ya gabata ne, wani mai suna Arthur Wagner dake zaman daya daga cikin kasuguman makiya Musulmai wanda ya dade yana bayyana kyamar sa akan addinin Islama tare da yin yunkurin hana gina masallatai, ya furta kalmar shahada.

Addinin Allah: Musuluntar shugaban jam'iyyar makiya Islama ta firgita duniya

Addinin Allah: Musuluntar shugaban jam'iyyar makiya Islama ta firgita duniya

KU KARANTA: 2019: Dole ayi wa 'yan takara gwajin lafiya

Legit.ng dai ta samu cewa wannan babban lamarin mai matukar ban mamaki yarazanar makiyan na Musulmai a dukkan fadin duniya tare da haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumuntan duniya.

A wani labarin kuma, Babbar hukumar nan dake kula da jin dadin mahajjata tare da kula da mahajjatan watau National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) a turance ta fitar da wani sakamakon tantancewa da suka yi wa kamfanonin jigilar mahajjatan shekarar bana.

Sakamakon dai na tantancewar da ya fito ya amince da kamfanoni tis'in sannan kuma ya yi fatali da wasu kamfanonin akalla hamsin da hudu duk dai game da jigilar mahajjatan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel