Masarautar kasar Saudiyya ta sake kashe wasu 'yan arewacin Najeriya 2
Kimanin watanni hudu kacal bayan mahukunta a kasar Saudiyya sun kashe wani dan Najeriya bisa laifin yin fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasar su, yanzu ma kasar ta sake kashe wasu karin mutane biyu bisa irin laifin.
Mun samu dai cewa yanzu haka cikin wasu 'yan Najeriyar da ke daure a kasar su kimanin mutam sha biyar ya duri ruwa suna jiran na su hukuncin musamman ma ganin yadda 'yan uwan nasu suna kare.
KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su hana ni zuwa Kano ba - Kwankwaso
Legit.ng haka zalika ta samu cewa wadanda aka kashe din a satin da ya gabata dukkanin su sun fito ne daga arewacin kasar Najeriyar kuma sunayen su Ibrahim Ciroma da kuma Maimudu Issah.
A wani labarin kuma, Babbar hukumar nan dake kula da jin dadin mahajjata tare da kula da mahajjatan watau National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) a turance ta fitar da wani sakamakon tantancewa da suka yi wa kamfanonin jigilar mahajjatan shekarar bana.
Sakamakon dai na tantancewar da ya fito ya amince da kamfanoni tis'in sannan kuma ya yi fatali da wasu kamfanonin akalla hamsin da hudu duk dai game da jigilar mahajjatan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng