Jaraba: Maganin karfin maza ya kusa aika wasu lahira

Jaraba: Maganin karfin maza ya kusa aika wasu lahira

- A kasar Zambiya, wasu samari su uku sun kamu da muguwar cutar amai da gudawa, bayan da suka sha maganin da suke tsammani zai kara musu karfi yayin sabgar bariki

- Kasashen Afirka dai sun dade suna sayar da magunguna irin wadannan na soyayya, babu kuma abin da suke so irin ace su jarumai ne a gadon soyayya

- Inda zaka ga masu motoci musamman a arewacin Najeriya, suma suna adin kalaman batsa ga lasifika ba kunya, kuma mutane su zo su saya

Jaraba: Maganin karfin maza ya kusa aika wasu lahira
Jaraba: Maganin karfin maza ya kusa aika wasu lahira

A kasar Zambiya, wasu samari su uku sun kamu da muguwar cutar amai da gudawa, bayan da suka sha maganin da suke tsammani zai kara musu karfi yayin sabgar bariki.

Daga farko dai an yi tsammanin sun kamu da kwalara ne sai daga baya aka gano cewa magungunan kara karfin mazan ne suka yi musu illa.

Tun a shekarar da ta gabata ne kasar Zambiya ke fama da matsananciyar annobar kwalara da ta yi sanadin kashe mutum 70, inda aka samu wadanda suka kamu da ita fiye da 3,000.

Amma akwai alamun cewa mutum ukun wadanda 'yan yankin gabashin kasar ne, ba sa daga cikin masu fama da annobar

DUBA WANNAN: Yadda mau sane suke sata daga bankinku

A maimakon haka, sai aka gano cewa sun yi ta dirkar maganin karfin maza ne wanda ake kira da mvubwe.

Babban jami'in gwamnati na yankin Chanda Kasolo, ya shaidawa BBC cewa, nan da nan mutanen suka fara amai inda aka garzaya da su cibiyar masu kula da kwalara.

Kasashen Afirka dai sun dade suna sayar da magunguna irin wadannan na soyayya, babu kuma abin da suke so irin ace su jarumai ne a gadon soyayya.

Inda zaka ga masu motoci musamman a arewacin Najeriya, suma suna adin kalaman batsa ga lasifika ba kunya, kuma mutane su zo su saya

An samo wannan labari ne daga BBC Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel