An damke dan Boko Haram a kasar Jamus, sunanshi Amaechi

An damke dan Boko Haram a kasar Jamus, sunanshi Amaechi

Jami’an tsaro a kasar Jamus sunyi ram da wani da ake zargin dan Boko Haram daga Najeriya a Turai.

An damke dan ta’addan mai shekaru 27 a ranan Laraba, 24 ga watan junairu a birnin Bavaria.

Bayan awa 24, kotu ta bada umurnin garkameshi a kurkuku.

Alkalin yace: “Babban mamban kungiyar yan tada kayan bayar Boko Haram ne”.

An damke dan Boko Haram a kasar Jamus, sunanshi Amaechi
An damke dan Boko Haram a kasar Jamus, sunanshi Amaechi

Dan ta’addan ya bayyana cewa ya shiga kungiyar ne a shekarar 2013 kuma ya bayyana cewa ya taka rawar gani wajen wasu manyan hare-hare da kungiyar ta kai kan al’umma Arewa maso gabas da Najeriya.

KU KARANTA: Rikicin makiyaya a jihar Binuwai: Gwamna Ortom ya caccaki ministan tsaro na Najeriya

An tuhumce shi da kisan mutane da dama a wasu hare-hare biyu da ya aki makarantu da kuma wani kauye inda kungiyar sukayi garkuwa da yan matan makaranta kuma suka kona coci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng