Hukumomi sun karyata wani bidiyo da ke nuna wai Fulani ne ke far wa mutane a Kudancin kasar nan
- Ana rade-radin fada a jihar Delta
- Wai makiyaya sun iso jihar a kwale-kwale
- Hukumar 'yansanda ta karyata lamarin
A jihar Delta, ana ta yada wani bidiyo da rade-radin wai fulani sun mamaye babban birnin jihar na Asaba, inda kowa ya shiga tsoro.
A labarin, wai ai sun iso birnin ne rafin kwara, wai cikin jiragen ruwa, domin kisan kare-dangi da mamaya.
Hukumar 'yansanda dai ta karyata wannan batu, inda ta kira shi da kanzon kurege, kakakin hukumar Andrew Aniemeka ya fadi.
DUBA WANNAN: Dubi me Buhari yake so yayi da biliyoyin kudade da ya tara
A cewarsa, 'kashe-kashe da rade-radin wai mahara sun iso da muggan makamai, a kwale-kwale har ukku, wanda ake yadawa a bidiyo a soshiyal midiya, karya ne'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng